Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Bayan fito na fito, mutanen gari sun yiwa ƴan bindiga lilis a Kano
Rahotanni daga unguwar Yamadawa Ɗorayi Babba da ke ƙaramar hukumar Gwale a nan Kano, na cewa, al’ummar unguwar sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin ƴan bindiga ne.
Shaidu sun ce, Al’amarin ya faru ne a cikin daren Laraba, bayan da mutanen biyu suka yi ƙoƙarin yin awon gaba da wani magidanci ta hanyar razana shi da bindiga a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gidan sa a mota.
Daga nan ne kuma magidancin yayi nasarar arcewa, inda jama’ar dake wajen suka ankara, inda suka afkawa ƴan bindigar.
Shaidun suka ci gaba da cewa, ƴan bindigar sun fara harbe-harbe, har suka ƙwace wani baburin adaidaita sahu, tare da ƙoƙarin guduwa da shi.
Amma duk da haka dandazon jama’ar gari sun cafke su, tare da miƙa su ga ofishin ƴan sanda na Ɗorayi Babba.
Wani cikin mazauna unguwar da suka cafke ƴan bindigar ya shaidawa Freedom Radio cewa, ƴan sanda sun garzaya da ƴan bindigar zuwa asibiti acikin daren sanadiyyar raunukan da mutane suka yi musu.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi ƙarin bayani a kai ba.
You must be logged in to post a comment Login