Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sauke Bashir Lado daga shugabancin hukumar NAPTIP

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar yaƙi da safarar bil’adam ta ƙasa NAPTIP Bashir Garba Lado.

Sauke Garba Lado na zuwa ne watanni huɗu bayan naɗa shi a matsayin shugaban hukumar.

Wannan na cikin sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya maye gurbin Garba Lado da Hajiya Fatima Waziri nan ta ke.

Kuma an naɗa Fatima biyo bayan yabawa da ministar jin ƙai Hajiya Sadiya Umar Faruk ta yi da ƙoƙarin ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!