Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Ganduje ya bai wa ƴan makaranta hutun sallah

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa ɗaliban makaranta hutun bikin ƙaramar sallah.

Hakan na cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa Gwamnan Kano kan harkokin ilimi Jilani Almustapha Ɗanmalam ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, hutun zai fara daga ranar Talata 11 ga watan Mayu da muke ciki zuwa Litinin 17 ga watan.

Ɗaliban makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi 16 ga wata, yayin da na jeka ka dawo kuma za su koma a ranar 17 ga wata.

Sanarwar ta ja hankulan iyayen yara kan su tabbatar ɗalibai sun koma makarantu a ranakun da aka sanya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!