Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi- Majalisar dokoki ta dakatar da Muhyi Magaji

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban hukumar karɓar ƙorafin da yaƙi da cin hanci da rashawa Muhyi Magaji Rimin Gado.

Majalisar ta ce ta dakatar da shi har tsawon wata guda domin samun damar yin bincike a kan sa.

Dakatarwar ta biyo bayan wasiƙr ƙorafin da ofishin babban akanta na jihar Kano ya aike wa majalisar bisa ƙorafin cewa shugaban hukumar yaƙi karɓar akantan da aka kai ofishin sa kamar yadda yake a tsarin dokar jihar Kano.

Haka kuma wasiƙr ta bayyana cewa shugaban hukumar ya naɗa mutumin da yake kan matakin albashi na 4 a matsayin akanta a hukumar maimakon wanda aka tura masa.

Bayan kammala karanta wasiƙr ne sai shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari ya buƙaci majalisar da ta dakatar da shi tare da miƙa ƙorafin ga kwamitin kula da hukumar domin gudanar da bincike.

Majalisar ta bai wa kwamitin tsawon makonni biyu domin ya gabatar mata da rahotonsu na binciken.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!