Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Da ɗumi-ɗumi – Sheikh Aminu Daurawa ya ajiye muƙaminsa na Babban Kwamandan Hisbah a Kano

Published

on

Babban Kwamandan hukumar Hisba a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye muƙaminsa.

Da safiyar ranar Juma’a ne Daurawa ya wallafa wani bidiyonsa da ya yi cikakken bayani kan ajiye muƙamin.

Cikin bidiyon an jiyo Daurawa na neman afuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa abin da yayi na kuskure yayin aikin sa a hukumar Hisba.

“Allah ya sa ni ba ni da wani ƙudiri illa naga matasa sun samu tarbiyya da gyara irin na Musulunci, hakan ne ya sa na rinƙa kiransu muna tattaunawa don samar da gyara, muna da aljihuna na rinƙa ƙoƙarin kyautata musu” a cewar Daurawa.

Ya kuma ce “Ina Kaduna na samu bayanan da Gwamna ya yi a kan aikin mu, kuma hakan ne ya sa na yanke shawarar ajiye muƙamina muka ina godiya da damar da ya bani”.

A ƙarshe Daurawa ya yi fatan alkhairi ga Gwamnan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!