Kaduna
Da ɗumi-ɗumi: El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, za a buɗe makarantun jihar daga ranar Litinin 19 ga watan Octoban da muke ciki, bayan shafe tsawon lokaci cikin hutu dalilin cutar Corona.
Kwamishinan ilimin jihar Dakta Shehu Makarfi ne ya bayyana hakan yau, yayin wani taron manema labarai.
Kwamishinan ya ce, ɗaliban da zasu koma makaranta sune ƴan aji shida na makarantar firamare dana aji biyu a ƙaramar sakandire sai kuma ƴan aji biyu na babbar sakandire.
A cewarsa gwamnati ta yi hakan ne domin bin dokokin likitoci wajen kare kamuwa daga cutar Covid-19.
Dangane da makarantun gaba da sakandire kuwa, kwamishinan yace, gwamnati ta bada umarnin a buɗe su, sai dai an buƙaci malamai kan su taƙaita karatun su ta hanyar amfani da ajujuwa da kuma fasahar zamani, domin rage cunkoson ɗalibai da ɗaukan tsawon lokaci a cikin makarantu.
Wakilin mu Haruna Ibrahim Idris ya rawaito kwamishinan Dr. Makarfi na cewa kawo yanzu suna kan tattaunawa da hukumar da ke kula da harkokin addinai ta jihar don samar da hanyar da ta dace wajen buɗe makarantun addinai.
You must be logged in to post a comment Login