Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna ɗaurin watanni shida
Kotun Majisitiri da ke filin jirgin saman Kano ta yanke hukunci ɗaurin watanni shida ba tare da zaɓin tara ba.
Yayin zaman kotun na yau Mai Shari’a Muntari Garba Ɗandago ya yanke mata wanann hukuncin ne bisa kalaman ɓatanci da ta yi ga wani mai suna Isah I. Isah a shafinta na Instagram.
Idan zaku iya tunawa dai a shekarar 2019 aka samu saɓani tsakanin Sadiyan da Isah.
Daga nan ne kuma ta yi masa kakkausan kalamai a cikin wasu faya-fayan bidiyo da ta riƙa wallafawa.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da Sadiyan ta sanar da cewa wasu na ƙoƙarin yin garkuwa da ita.
Sadiya Haruna ta yi fice a kafafen sada zumunta wajen yawan cece-kuce.
Ko a shekarar da ta gabata wata kotun ta yanke mata hukuncin komawa makarantar Islamiyya bayan da Hisbah ta zarge ta da bayyana tsiraici da sakin baki a kafafen sada zumunta.
You must be logged in to post a comment Login