Addini
Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin komawa Islamiyya
Yau Litinin rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wata mai amfani da kafafen sada zumunta Sadiya Haruna a gaban kotu.
An gurfanar da ita a kotun shari’ar Musulunci da ke hukumar Hisbah, bisa zargin yaɗa batsa a kafafen sada zumunta.
Yayin zaman kotun mai shari’a Ali Jibrin Ɗanzaki ya yanke mata hukuncin sanyata a makarantar Islamiyya ta Darul Hadith har tsawon wata shida.
Za ta riƙa zuwa kullum tare da rakiya jami’in hukuma.
Sannan za ta riƙa sanya hannu a duk sanda ta je.
Sadiya Haruna dai ta shahara a kafafen sada zumunta wajen yaɗa hotuna tare da kalaman batsa.
Tun da farko rundunar ƴan sandan jihar Kano ce, ta karɓi ƙorafi daga mutane kan ayyukan matashiyar.
You must be logged in to post a comment Login