Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokoki ta rushe masarautun Kano guda 5
Majalisar dokokin jihar Kano ta rushe ɗaukacin masarautun jihar guda biyar.
Majalisar ta yi hakan ne bayan da ta amince da gyaran dokar da ta kafa masarautun guda 5 a jihar.
Gyaran dokar ya yi tanadin cewa, Duk ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka soke ya zama rusasshe.
Haka kuma duk hakimai da aka daukaka ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan mukamansu na baya.
Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar Dala a zauren Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ne ya dauki nauyin gabatar da ƙudurin gyaran dokokin.
Yayin ganawarsa da manema labarai, shugaban masu rinjayen ya ce, a yanzu babu sarki a Kano sai wanda gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya naɗa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, cikin gyaran da aka yi an mayar da jihar Kano mai masarauta guda ɗaya, sai dai, nan gaba za a ƙirƙiri wasu masarautun masu Daraja ta biyu.
You must be logged in to post a comment Login