Labarai
Da ɗumi-ɗumi- Masarautar Kano ta dakatar da hawan sallah
Masarautar Kano ta dakatar da hawan sallah na al’ada da ake gudanarwa kowacce sallah.
Masarautar ta yanke hukuncin ne a zamanta na yau Litinin, ta bakin Madakin Kano Alhaji Yusuf Labahani.
a cewar sa, dakatarwa ta biyo bayan rahoton sake bullar annobar corona karo na uku da aka yi a kasar nan, wanda hukumomin lafiya ke shawartar daukan matakin kare yaduwar ta.
Masarautar na bukatar al’ummar jihar Kano da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya.
kan wannan batu kuma gwamnatin jihar Kano tayi karin bayani kan matakin dakatar da hawan sallar, ta bakin kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba.
“Mun samu umarni daga gwamnatin tarayya na dakatar da hawan sallah, sakamakon yadda rahotanni suka nuna cewa jihar Kano na cikin jihohi shida da ake fargabar ɓarkewar annobar corona karo na shida” inji Muhammad Garba.
Malam Muhammad Garba ya kuma ce, umarnin bai shafi sallar idi ba, sai akwai bukatar mutane su dauki matakin kare kai don kiyaye yaduwar ta.
You must be logged in to post a comment Login