Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Fiye da wata hudu ba a samu mai dauke da cutar corona ba a Sokoto

Published

on

Gwamnatin jihar Sokoto, ta sanar da cewar ba a samu bullar Annobar cutar Corona a fadin jihar na tsawon kwanaki 123.

Kwamishinan lafiya na jihar ta Sokoto Dr. Muhammadu Ali Inname, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai kan halin da ake ciki dangane da yaki da cutar.

Dr Inname, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar Corona na jihar yace kawo yanzu haka tun bayan wanda aka samu a baya suna da cutar su 775, tsawon kwanakin da aka shafe na 123 a jihar ba samu wanda suka kara kamuwa da cutar ba, da hakan ke nufin an samu raguwar cutar.

Kwamishinan, ya kara dacewa gwamnatin jihar ta yiwa mutum 17,440 a fadin jihar gwajin cutar ta Corona, a bangare daya kuma ta amince da kashe kudi sama da Miliyan 500, don siyar magungunan zazzabin Malaria.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!