Labarai
Da Dumi-dumi: Hisbah ta hana jin wakar Hamisu Breaker

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da hana sauraron wata sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna Amanata.
Mataimakiyar Babban Kwamandan hukumar ta Hisbah a ɓangaren Mata Dakta Khadija Sagir, ce ta bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ta aiko wa Freedom Radio a yau Alhamis.
Dakta Khadija Sagir ta ce, waƙar ƙarara ta na nuna zina tare da nuna cewa mai yinta ya na cikin halin maye.
Ta kuma ce, sun gano faya-fayan bidiyo da suke nuna yadda mata ke daukar bidiyo suna bin wakar tare da yin lanƙwashe-lanƙwashe da karya murya.
Haka kuma hukumar ta yi kira ga matasa su ƙaurace wa sauraron waƙar ta Amanata wadda mawakin Hamisu Breaker , ya rera, don kuwa a wajen hukumar sauraron wannan waƙa haramun ne.
Latsa Alamar Play domin jin muryarta
You must be logged in to post a comment Login