Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Hisbah ta cafke yaron da ya biyo Ado Gwanja daga Adamawa

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani kankanin yaro mai suna Abdullahi Muhammad dan asalin karamar hukumar Shelang ta jihar Adamawa, wanda ya zo Kano domin haduwa da fitaccen mawakin nan Ado Isa Gwanja.

Abdullahi Muhammad mai shekaru goma ya biyo motar gawayi daga garin Shelang har zuwa nan Kano, ba tare da sanin iyayen sa ba.

Wakilin mu Yusuf Ali Abdallah ya rawaito mana cewa, jami’an Hisba sun dakume yaron kafin ya samu ganawa da Ado Gwanja.

Gwani Murtala Mahmud shi ne kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kumbotso ya ce, yanzu haka suna shirye-shirye domin mayar da wannan yaron zuwa ga hannun iyayen sa.

Ku kasance da shirin Inda Ranka @7am don jin yadda wannan yaro ya rerawa shirin Inda Ranka wata wakar sa.

Karin labarai:

Hisbah ta gano maganin Coronavirus

Hisbah ta kama mai yiwa mata kunshi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!