Connect with us

Labarai

Da dumi-dumi: Shekarau ya fice daga NNPP zuwa PDP

Published

on

Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP.

Malam Shekarau wanda  tsohon gwamnan ne ya bayyana ficewar ta sa, yayin wani taro na musamman da ya gudanar a gidan sa dake mundubawa yau Litini.

Tuni dai Malam Ibrahim Shekarau din ya samu tarba daga dan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar ta PDP Alhaji Atiku Abubakar wanda ya zo Kano domin karbarsa.

Da yake yi masa maraba a jam’iyyar, Atiku Abubakar ya ce, shigowar yan siyasa irin su Shekarau a jam’iyya babbarb nasara ce da kuma ci gaban jam’iyyar.

Idan za a iya tunawa dai Malam Ibrahim Shekarau bai dade da yiwa jam’iyyar NNPP mubaya’a ba, sai kuma ya sake sauya sheka zuwa PDP sakamakon abin ya kira rashin adalci a jam’iyyar NNPP.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!