Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Da gaske za ayi gwajin maganin Corona a Kano?

Published

on

Ana ta yada wani labari a kafafan sada zumunta na cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta zabi jihar Kano kadai domin yin gwajin maganin cutar Covid-19 da ta addabi duniya, sai dai wannan labarin ba haka yake ba.

Gaskiyar lamari:

Ministan lafiya na kasa Osagie Ehanire ya sanar da cewa Najeriya ta amince da shiga tsarin gwajin magunguna da hukumar lafiya ta duniya WHO ke gudanarwa cikin kasashen sama da dari.

Ministan ya bayyana hakanne a yayin zaman kwamitin karta kwana kan yaki da cutar na kasa a ranar Litinin.

Ehanire ya ce gwamnatin tarayya ta bada jihohi biyar da birnin tarayya Abuja, wadanda suka hada da jihar Legas da jihar Ogun da jihohin Kano da Kaduna da kuma jihar Sokoto domin yin gwajin magungunan.

Sai dai har zuwa yanzu ba a sanar da lokacin fara wannan gwaji ba.

Karin bayani:
1. Ba WHO ce ta zabi Kano cikin jihohin da zata yi gwaji ba.
2. Ba Kano ce jiha kadai da gwamnatin tarayya ta bayar domin yin gwajin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!