Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da kudaden ma’adinai ‘yan ta’adda ke sayan makamai – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta gano cewa ‘yan ta’adda suna amfani da haramtattun kudade da suke samu wajen hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wajen sayo makamai da suke aikata ta’addanci a sassa daban-daban na kasar nan.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a jiya talata lokacin da ya ke bude bikin kasa da kasa don nuna ma’adinai wanda ke gudana a birnin Badun babban birnin jihar Oyo.

Shugaban kasar wanda ministan ma’adinai Dr. Uchechukwu Ogah ya wakilta ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen kare lafiya da dukiyar al’ummar kasar nan.

Shugaban kasar ya ce tun da gwmanatinsa ta gano wannan lamari shi ya sanya ta dauki matakin da ya dace.

‘‘Yan ta’adda suna shiga kauyuka wuraren da ake hakar ma’adinai suna aiki ba bisa ka’ida ba, kudaden da suke samu sai su je su sayi makamai da shi’’ a cewar shugaban kasar’’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!