Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

‘Yan bindiga sun bude wa jerin gwanon motocin Sarkin Birnin Gwari wuta

Published

on

‘Yan bindiga sun bude wuta kan jerin gwanon motocin mai martaba sarkin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna Alhaji Zubairu Jubril Mai Gwari II

 

Rahotanni sun ce an kai hari kan kwambar motocin sarkin na Birnin Gwari ne akan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da yammacin jiya talata.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, direbar sarkin na Birnin Gwari Umar Jubril ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, sarkin ba ya kusa da inda ‘yan bindigar su ka kai harin.

 

‘‘Yan bindigar sun turo reshen bishiya akan titin da nufin tare jerin gwanon motocin sarkin, wanda kuma da suka gaza tare mu ne, sai kawai su ka bude mana wuta’’.

‘‘Ba mu tsaya ba, sun yi kokarin samu na da bindiga, amma Allah ya kiyaye ni, alburushi ya wuce ta kai na’’ inji Umar Jibril.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!