Labarai
Daga Faransa: Buhari zai wuce Afrika ta Kudu
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar birnin Faris na ƙasar Faransa zuwa birnin Durban na ƙasar Afrika ta Kudu.
Shugaban zai je Afrika ta Kudu ne bisa gayyata ta musamman da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi masa, domin halartar bikin buɗe taron baje kolin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka karo na 2 na shekarar 2021 wanda zai gudana a 15 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan Nuwamban.
Buhari ya isa ƙasar Faransa don ganawa da Macron
Hakan ba cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar a ranar Asabar.
Shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin Waje Geoffrey Onyeama da ministan masana’antu ciniki da zuba jari, Otunba Niyi Adebayo da darakta janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.
Sai babban Darakta kuma babban jami’in hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya, Segun Awolowo.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar Talata 16 ga watan Nuwamba.
You must be logged in to post a comment Login