Labarai
Daga ranar 1 ga watan Mayu za a daina ganin dogwayen layuka a gidajen man fetur: NNPCL
Kamfanin man fetur na kasa NNPC ya ce daga gobe Laraba da Daya ga watan Mayu za a daina samun dogayen layuka da ake samu a gidajen man kasar nan.
Shugaban sashin sadarwa na kamfanin Mr Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Talata 30 ga watan Afrilun 2024 a Lagos.
Mr Olufemi Soneye, ya kuma ce, yanzu haka kamfanin zai ya kara yawan litar man fetur din da yake fitarwa zuwa Miliyan daya da dubu dari biyar domin rabawa gidajen man a fadin kasar nan da hakan zai sa a rage samun dogayen layukan da kuma samun wahalar sa.
Ya kuma ce za a dauki kwanaki uku ana raba man zuwa ga sassa daban daban na kasar nan.
Haka kuma ya ce kamfanin ya lura da yadda wasu daga cikin gidajen man fetur din suke amfani da wahalar man da ake samu wajen siyar da shi yadda sukaga dama.
A domin haka yake cewa tsakanin yau da gobe man fetur din zai wadata a gabaki dayan kasar nan.
Kusan makonni biyu kenan ana fama da samun Dogayen Layuka a gidajen man fetur sakamakon karancin sa da ake samu inda ake samun mabanbantan ra’ayoyi a tsakanin gidajen man, hakan kuma ya haifar da karin kudin sufuri da kuma wahalar ababen hawa a nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login