Connect with us

Labarai

Dakarun Operation Fansan Yamma sun hallaka ƴan bindiga 21 a dajin Shawu

Published

on

Dakarun rundunar sojin Najeriya na Operation Fansan Yamma sun hallaka wasu ƴan bindiga 21 a dajin Shawu  da ke  yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

 

Ta cikin wata  sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, rundunar sojin ta ce, dakarun na Operation Fansan Yamma sun samu nasarar kashe ƴan bindigar ne bayan kai musu hari a maɓoyarsu ranar 23 ga watan nan da muke ciki na Mayu, a ci gaba da yaƙi da ayyukan ɓata-garin.

 

Sanarwar ta ce an samu nasarar kashe ƴan bindigar ne bayan artabu na tsawon lokaci, ciki har da waɗanda kogi ya tafi da su lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.

 

Rundunar ta  kuma ce an ƙwato makamai da harsashai da dama ciki har da babura 40 da shanu da dama waɗanda ƴan bindigar suka sace.

 

Har ila yau, sojojin sun ce samamen da suka kai ya sa ƴan bindigar tserewa tare da barin sansaninsu, inda suka fantsama cikin dazuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!