Labarai
Dakarun Operation Fansar Yamma sun ceto mutane 50 da shanu 32 daga hannun yan Bindiga

Rundunar Sojin kasar nan ta Operation Fansar Yamma ta ceto wasu mutane 50 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tare da ƙwato shanu 32 da aka sace a ƙauyen Raudama, da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
A cewar sanarwar, an sace mutanen ne ranar Lahadin da ta gabata lokacin da ’yan bindigar suka kai farmaki ƙauyen inda suka sace mutanen da kuma shanun.
Kwararren masanin nan a fannin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama, ya bayyana cewa, wasu majiyoyi sun shaida masa cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
Haka kuma,ya ce, bayan harin, sojoji da ’yan sanda sun haɗa runduna ta musamman da ta bi sawun ’yan bindigar, inda suka fafata da su.
Daga bisani ne dakarun suka samu nasarar fatattakar ’yan bindigar, tare da ceto mutanen da aka sace, hade da ƙwato shanun.
You must be logged in to post a comment Login