Connect with us

Labarai

Dakarun Operation Sahel Sanity sun kashe ‘yan bindiga a Zamfara

Published

on

Dakarun operation Sahel Sanity na rundunar sojin kasar nan da ke aikin samar da tsaro a yankin arewa maso yammacin kasar nan, ta ce, ta kashe wasu ‘yan bindiga guda uku a jihohin Katsina da Zamfara.

A cewar rundunar ta kuma kama wasu mutane goma da ake zargin ‘yan bindiga ne da kuma masu kai musu tsegumin abinda ke faruwa a gari.

Mai magana da yawun dakarun kasar nan da ke bakin daga, Burgediya janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Katsina.

Sanarwar ta ce, a ranar goma sha shida ga wannan wata ne dakarun na Operation Sahel Sanity yayin wani rangadi a dajin Dumburum suka kashe ‘yan bindigar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,999 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!