Labarai
Dakatar da layukan sadarwa ya rage yawan hare-hare a jihar Zamfara
A kwana-kwanan nan ne jihar Zamfara ta ɗauki sabbin matakai domin yaƙi da matsalar tsaro ciki kuma har da rufe layukan waya.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya bayyawa Freedom Radio cewa matakin toshe layukan wayar, zai sa ƴan bindigar a mawuyacin hali, ta yadda jami’an tsaro zasu samu damar zaƙulo ƴan ta’addan.
Matawalle ya ce “lalle an samu cigaba ƙwarai da gaske tunda har an, raunata wasu an kuma kashe wasu, kuma nan bada dadewa ba za’a kawo ƙarshen duk wasu hare-hare a fadin jihar”.
Wani mazauni yankin karkara daga ƙaramar hukumar Tsafe, mai suna Bashar Fegin Ɗanmarke ya ce “ kusan sati guda kenan yanzu mun samu nutsuwa da kwanciyar hankali.”
Shima wani direba mai suna Nura Ibrahim ya ce lallai dokokin sunyi tasiri ƙwarai da gaske, tunda gashi har ƴan bindikar sun sallamo mutanan su kusan su ashirin ba tare da an basu ko sisi ba.
You must be logged in to post a comment Login