Labarai
Dalibai fiye da dari uku sun sami tallafin karatu-Sha’aban
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar birni da kewaye a majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin kula da al’amuran tsaro na majalisar Sha’aban Ibrahim Sharida ya ce ya dauki nauyin dalibai fiye da dari da zasu je kasashen wajen don karu karatu.
Sha’aban Ibrahim ya bayyan hakan a cikin shirin barka da hantsi na nan tashar Freedom Radio wanda ya mai da hankali kan yadda yake gudanar da ayyukan sa bayan ya kama aiki a matsayin sa na shugaban kwamitin tsaro.
Dan majalisar ya ce a halin yanzu an kammala komai na dalibai fiye da saba’in wanda za su bar gida Najeriya don zuwa kasashen wajen don yin nazari a bangarori daban-daban na ilimi.
Haka zalika Sha’aban Ibrahim a gefe guda ya ce kwamitin sa na kokarin inganta tsaro a sassan kasar nan yana mai cewa a shirye yake ya kawo karshen ‘yan ta’adda da ayyukan bata gari da suka addabi kasar nan.
Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam
Tsofaffin dalibai: Za mu tallafa wa jami’ar Bayero
Da yake magana akan batun ceto yara tara ‘yan asalin jihar Kano da aka sace aka saida su a jihar Anambra, dan majalisar ya ce nan bada jimawa kwamitin tsaro na majalisar zai kawo karshen yin garkuwa da mutane da kuma sace-sace yara da ake fuskanta a Arewacin kasar nan.