Labarai
NELFUND ta bayyana dalilanta na dakatar da tura wa ɗalibai kuɗi

Hukumar bada Lamunin Ilimi ta Najeriya NELFUND, ta tabbatar da cewar an samu matsala ta fasaha da ta samu a shafin ta na Internet da ya haddasa tsaiko wajen biyan kuɗaɗen ɗalibai, lamarin da ya sa dubban waɗanda suka ci gajiyar shirin suka shafe kusan watanni biyu ba tare da karɓar kuɗinsu ba.
Wata majiya daga cikin NELFUND ta tabbatar da faruwar lamarin da ta ce hukumar na ƙoƙarin gyara tangardar da kuma daidaita bayanan biyan kuɗaɗen da abin ya shafa.
Ƙungiyar Ɗalibai ta kasa (NANS) ta ce ta samu korafe-korafe da dama daga ɗalibai a cibiyoyin ilimi daban-daban na ƙasar kan jinkirin biyan kuɗaɗen , da shugaban ƙungiyar, Babatunde Akinteye, ya bayyana cewa bayanan da suka tattara sun nuna cewa an dakatar da biyan kuɗaɗen kula da kai na ɗalibai tsawon watanni biyu ba tare da cikakken bayani daga hukumomin da abin ya shafa ba.
Akinteye ya buƙaci Manajan Daraktan asusun na NELFUND, Akintunde Sawyerr, da Ministan Ilimi, Tunji Alausa, da Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, da su sa baki domin tabbatar da biyan dukkan kuɗaɗen da ake bin ɗaliban ba tare da ƙarin jinkiri ba.
You must be logged in to post a comment Login