Connect with us

Labarai

Wasu ‘yan bindiga sun kashe malamin Jami’a a Abuja

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a ko waye ba sun hallaka wani malami a jami’ar tarayya ta Birnin Kebbi a jihar Kebbi Abdullahi Abubakar Dakingari.

‘Yan bindigar sun harbe shi ne a unguwar Life Camp Quarters da ke birnin tarayya Abuja da karfe 10:30 na daren llarabar da ta gabata, lokacin da ya je duba mahaifinsa da ke kwance a asibiti a Abuja.

Wani dan uwan mamacin mai suna Abubakar Mu’azu Dakingari ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 38, kuma ya bar mace guda da ‘da daya.

Tuni aka binne Abdullahi Abubakar a garin Dakingari kamar yadda addinin musulunci ta tanada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!