Connect with us

Labarai

Mun zuba jarin Naira biliyan 120 a masaku da masana’antun jima – CBN

Published

on

Babban Bankin Kasa (CBN) ya ce ya zuba jarin Naira biliyan120 a harkokin masaku da masana’antun jima da sarrafa auduga.

Mataimakin gwamnan bankin na CBN, Mista Edward Lamatek Adamu ne ya bayyana hakan a jiya, ya yin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin masana’antun sarrafa auduga  a Abuja.

Bankin na CBN ya kuma ce a shekarar nan da muke ciki bankin yana kokarin noman auduga tan 300,000 don inganta masana’antun tufafi a kasar nan.

Mista Edward Adamu ya kara da cewa, kokarin da aka yi, ya haifar da karuwar masana’antun sarrafa tufafi a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!