Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da suka sanya Burtaniya zata tallafawa Najeriya da abinci

Published

on

Kasar Burtaniya ta ce ta fitar da Yiro miliyon bakwai ga al’ummar Najeriya domin samar da abinci mai gina jiki da ruwan sha mai tsafta da muhalli mai kyau ga marasa karfi.

Haka zalika kasar ta Burtaniya ta ce ta fitar da karin fam miliyan arba’in da bakwai na tallafi ga mutanan da basu dashi a kasashe guda tara dake fadin Duniya.

Tallafin dai ana saran zai isa ga mutum dubu dari hudu da talatin na ‘yan Najeriya a shekarar da muka shiga ta 2021.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da mataimakin babban jami’in kasar Burtaniya a jihar Legas ya fitar a jiya Alhamis.

Sanarwar ta ce kasar ta Burtaniya na neman masu hannu da shuni na kasa da kasa da su samar da karin kudaden wajen dan tallafawa kasashen da ke cikin kangin talauci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!