Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Dalilan da suka sanya mace ta auri maza biyu a Kano

Published

on

Wani mutum mai suna Bello Ibrahim, ya yi korafi akan matarsa Hauwa’u Aliyu wacce ya ce, su na zaune a cikin kwanciyar hankali har ta kai sun haifi ‘ya’ya 6, daga bisani rashin lafiya ta kama shi wadda ta kai ga mayar dashi gida kauye domin samun cikakkiyar kulawa, ita kuma Hauwa’u sai ta yi zamanta a birni domin kulawa da ‘ya’yan da suka haifa.

Bayan Malam bello ya sami sauki, sai ya koma gidansan wajen matarsa inda ya yi kacibus da wani mutum kwance ya yi dai-dai akan gadon matarsa, har ya yi kururuwar nemo Sungumi, sai ya ga cewar, ko kadan wannan bako bai tsorata ba, har ma yake tambayar Malam Bello cewar, lafiya ya shigo gidan matarsa haka ba sallama ba neman izni.

Malam Bello ya shiga dogon tunani har rigima ta turnuke kowa na ikirarin cewar, matarsa ce, inda ita kuwa matar ta tsaya ta na tauna cingam abin ta ta na kallonsu.

Daga nan ne Malam Bello ya garzaya hukumar Hisba ta karamar hukumar Kumbotso, bayan an gayyato kowanne bangare sai kowa ya tsaya kai da fata cewar, Hauwa’u iyalinsa ce ta sunna, har ma shi sabon angon ya ke nuna cewar, auren nasu har da ciki da goyo.

A karshe dai hukumar Hisbah ta ce, sai an je Shalkwatar hukumar, kamar yadda Kwamandan na Kumbotso Gwani Murtala Mahmud Yunusa ya bayyana.

A zantawar wakilinmu da Yusuf Ali Abdallah da matar Hauwa’u mai maza biyu ta bayyana cewar, hakika ta shaida mijinta na fari Malam Bello, kuma shi ne ya haifi yaya 6, sai dai ta ce gargarar rashin lafiya ya sawwake mata.

Sai dai Malam Bello ya musanta zancen ya na mai cewar, yaushe ya sake ta? ya kuma shaida cewar bai taba sakin matar ta sa ba, idan ma da gaske take ina takardar saki?

Nazari kan halin da yaran da aka haifa bata hanyar aure ba

Bana neman matar Aure-BABANGIDA

Hukumar Hisbah ta gana da saurayin dake shirin auren Ba’amurkiya

Sh ikuwa angon baya, Bala Abdusalam ya ce, kallo daya ya yi wa matar ta sa bisa ka’ida, bayan da ya kamu da soyayyarta, sai ya nemi aurenta kuma kuma ya biya sadaki Naira Dubu 20, ya ba ta a matsayinsa na direban babbar mota ya na ba ta sai yayi lodin Adamawa ya tafi, bai waiwayo ba sai da ta kira shi a waya ta shaida masa cewar, an gama komai ta kuma ce masa shaidun ma sun shaida, shi kuwa tun daga Adamawa ya tanadi Zabin sa gasassu ya kunso ya tare a dakin amarya, kuma gashi zaman ya yi dadi har da ciki da goyo.

Wakilin namu ya tambayi Bala Abdusalam wato sabon angon, shin ya aika waliyansa tunda magana ake ta aure bayan sadaki akwai siga? Sai ya ce, shi komai da komai ya hade mata amma yanzu ya gane akwai matsala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!