Labarai
Dalilin da suka sa Ganduje zai kashe Naira miliyan 880 don gyaran makarantun Boko
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata kashe fiye da Naira miliyan 880 domin gyara wasu makarantun firamare a kananan hukumomi 44 na jihar nan.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan lokacin da yake Mika takardar cekin kudi na miliyan 20 ga kwamitin cigaban ilimi na kananan hukumomi 44
Ya Kara da cewa an zayyana kowanne irin aikin da za’ayi a kowacce makaranta sannan za’a aiwatar da aikin ne cikin makwanni uku
Da yake jawabi shugaban hukumar ilimin bai daya na Kano Dr Danlami Hayyo Ya ce, “Wannan kudade an sadaukar da su ne domin inganta harkoki ilimi a wani bangare na cigaban ilimi a jihar Kano wanda yake kyauta Kuma dole”.
Anasa bangaren sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero kira ya yi ga kwamitocin wajen tabbatar da anyi aiki Mai kyau da inganci.
Yana mai cewa, “ilimi shi ne kashin bayan cigaban kowacce al’umma a don haka ya zama wajibi gwamnatoci su baiwa wannan bangaren fifiko”
Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa shugaban jami’ar Bayero ya gabatar da mukala kan muhimmancin ilimi kyauta kuma dole.
You must be logged in to post a comment Login