Connect with us

Labarai

Dalilin da suka sa Ganduje zai kashe Naira miliyan 880 don gyaran makarantun Boko

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata kashe fiye da Naira miliyan 880 domin gyara wasu makarantun firamare a kananan hukumomi 44 na jihar nan.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan lokacin da yake Mika takardar cekin kudi na miliyan 20 ga kwamitin cigaban ilimi na kananan hukumomi 44

Ya Kara da cewa an  zayyana kowanne irin aikin da za’ayi a kowacce makaranta sannan za’a aiwatar da aikin ne cikin makwanni uku

Da yake jawabi shugaban hukumar ilimin bai daya na Kano Dr Danlami Hayyo Ya ce,  “Wannan kudade an sadaukar da su ne domin inganta harkoki ilimi a wani bangare na cigaban ilimi  a jihar Kano wanda yake kyauta Kuma dole”.

Anasa bangaren sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero kira  ya yi ga  kwamitocin wajen tabbatar da anyi aiki Mai kyau da inganci.

Yana mai cewa, “ilimi shi ne kashin bayan cigaban kowacce al’umma a don haka ya zama wajibi gwamnatoci su baiwa wannan bangaren fifiko”

Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano  Zahrau Nasir ta ruwaito cewa shugaban jami’ar Bayero ya gabatar da mukala kan muhimmancin ilimi kyauta kuma dole.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!