Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Dalilin da ya sa Al’ummar kasar Senegal shiga farin ciki bayan lashe gasar AFCON

Published

on

Al’ummar kasar Senegal na ci gaba da nuna farin cikinsu, bayan da tawagar kasar ta lashe gasar kofin kasashen afrika ta (AFCON)

Dubun dubatar al’ummar kasar ne sukai da fifi a babban birnin kasar na Dakar, tare da daga tutoci suna nuna farincikinsu bayan da kasarsu ta lashe gasar.

Cikin wadanda suka tarbi tawagar kasar harda shugaba Macky Sall, wanda ya halarci filin jirgin sama da ‘yan wasan tawagar suka sauka.

Yan wasan kasar Senegal lokacin da suke murnan zura kwallo a wasan karshe

Dan wasan Liverpool Sadio Mane ne dai shi ne ya zura kwallon da ta baiwa kasarsa ta Senegal damar lashe gasar da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaran gida akan kasar Masar (Egypt) a ranar Lahadi 06 ga Fabrairun 2022.

Wasan karshen da ya gudana filin Olambe dake a birnin kasar Kamaru Yaounde.

Nasarar lashe gasar da Senegal tayi shi ne na farko a tarihin kasar, wanda hakan yasa ‘yan kasar akalla mutane miliyan uku nuna farin cikinsu da nasarar, bayaga fitowa sassan kasar domin taya kasar tasu murna.

Ko a ranar Litinin da ta gabata gwamnatin kasar ta ayyana hutun kwana daya domin taya tawagar murnan lashe gasar.

Sadio Mane

Senegal da ke a mataki na farko a jerin kasashe a nahiyar afrika, ta kai wasan karshe har sau biyu a baya, inda a shekarar 2019 ma tayi rashin nasara a wasan karshe a hannun kasar Algeria da ci 1-0.

Hakama a shekarar 2002 tayi rashin nasara a wasan na karshe a hannun kasar Kamaru a bugun daga kai sai mai tsaran gida.

Akalla ‘yan kasar daga sassa daban-daban ne dai sukai fitar dango domin taro tawagar ta Senegal bayan da suka isa kasar daga Kamaru da a nan aka gudanar da gasar.

Inda mutane suka fito birnin Dakar domin nuna farin cikinsu da kuma kauna bayan da kasarsu tayi nasarar lashe gasar ta AFCON karo ta 33.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!