Labaran Wasanni
Dalilin da yasa wasa tsakanin Manchester United da Liverpool ke daukar hankali a Duniya
A tarihin haduwar Manchester United da Liverpool sun hadu ne sau 202.
Inda Manchester United ta yi nasara kan Liverpool sau 81, yayin da ita kuma Liverpool ta samu nasara kan United din sau 68 sai kunnan doke da sukayi sau 53.
Liverpool dai itace babbar abokiyar hamayyar Manchester united a kasar Ingila.
Yanzu dai babu abin da Manchester ta saka a gabanta sama da ta dauki gasar cin kofin Firimiyar kasar Ingila a bana, yayin da ita kuma Liverpool ke kokarin ganin ta kare kambunta na daukar gasar ta shekarar 2020/2021 da ta gabata.
Manchester United dai ta samu nasara kan Liverpool a gasar Firimiyar ta Ingila sau 28 ta kuma zuba mata kwallaye a gasar sau 79, yayin da ita kuma Liverpool ta samu nasara kan United din sau 16 ta kuma zura mata kwallaye sau 67.
A wasan da kungiyoyin za su buga yau Lahadi 24 ga watan Octoban 2021, kallo zai koma kan Dan wasan United Cristiano Ronaldo dana Liverpool Muhammad Salah duba da irin gudunmawar da suke bawa kungiyoyin nasu.
You must be logged in to post a comment Login