Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

A karon Farko Liverpool ta lashe gasar Firimiyar Ingila cikin shekaru 30

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila ta lashe kofin Firimiyar kasar na kakar wasanni ta shekarar 2019/2020.

Nasarar daukan kofin na Liverpool a yau Alhamis ya biyo bayan rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta yi a daren Alhamis a hannun Chelsea daci 2-1.

Yanzu dai Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na da maki 86 a gasar yayin da Manchester City dake biye mata ke da maki 63, cikin wasanni 31 da aka buga a gasar.

Yanzu dai wasanni bakwai ya rage a karkare gasar ta Firimiyar ta Ingila, inda za’a buga wasanni 38.

Zuwa yanzu dai Liverpool ta bai wa Manchester City dake biye mata a matsayi na biyu tazarar maki 23.

Tsawon shekaru Talatin kenan rabon da Liverpool ta dauki gasar ta Firimiyar kasar ta Ingila.

A jiya Laraba ne Kungiyar ta Liverpool ta samu nasarar zura wa Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace kwallo 4-0.

A bana dai Liverpool ta samu nasarar cin wasanni 28 a gasar ta Firimiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!