Labarai
Allah ya yiwa Alh. Bello Isah Bayero rasuwa

Dan siyasar nan na jam’iyyar APC Alhaji Bello Isah Bayero ya rasu a daren ranar Alhamis.
Iyalan marigayin sun shaida wa Freedom Radio cewa, marigayin ya rasu ne a asibitin Aminu Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi Isah Bayero ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, ya bar mata 2 da ‘ya’ya 8.
A cewar iyalansa za a yi jana’izarsa bayan sallar Jumu’a a fadar Sarkin Kano.
A shekarar 2011 marigayin ya yi takarar sanatan Kano ta tsakiya sai dai bai samu nasara ba.
You must be logged in to post a comment Login