Wasanni
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya tafi jinya.
Marcus Rashford ba zai samu buga wasu wasanni da Manchester United zata kara ba, sakamakon rauni da ya samu a cinyarsa.
United bata bayyana iya adadin lokacin da dan wasan mai shekaru 25 zai dauka yana jinyar ba.
Rashford, ya zura kwallaye 28 a kakar wasa ta bana a dukkanin wasan da ya wakilci Manchester United.
Manchester zata kara da Sevilla a gasar Turai ta Europa a wasan dab da kusa da na karshe a ranar Alhamis a filin wasa na Old Trafford.
You must be logged in to post a comment Login