Labarai
Dangantaka tsakanin ingila da Kano, dadaddiyar alaka ce- Sarkin Kano
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace masarautar Ingila da masarautar jihar kano akwai alaka mai karfin gaske.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakoncin sabon jakadan kasar Ingila Richard Montgomery daya ziyarace shi a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace halakar najeriya da kasar ingila halaka ce mai tsawon tarihi tun zamanin sarkin kano marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero har zuwa wannan lokaci.
Sarkin ya kara da cewa dama dangartakan dake tsakanin kasashen biyu alakace wace baza’a iya mantawa da itaba.
sarki yayiwa jakadan fatan alheri musamman ma kan matsayin daya samu na jakadanci kasar ingila a najeriya.
Freedom Radio ta rawaito cewa yayin ziyarar da sabon jakadan kasar ingila ya kai fadar mai martaba Sarkin Kanon, ya tafi ne tare da tawagar ma’aikatasa.
Rahoton: Shamsu Dau Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login