Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abubuwan da suka faru a Katagum yayin ziyarar Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Katagum Alhaji Umar Faroq na biyu ya sha alwashin ganin ɗorewar kyakkyawar alaƙar masarautar sa da al’ummar Kano.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da maimartaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai masa a fadarsa.

Ziyarar dai na cikin jerin ziyarce-ziyarce da sarkin Kano ke gabatar wa don kara karfafa dangantakar masarautar Kano da sauran garuruwa.

Sarkin Kano yayin ziyarar da ya kai masarautar Katagum

Me sarkin Kano ya yi a ziyarar?
A yayin ziyarar dai Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci sallah da kuma zikirin jumu’a na wannan makon, a babban masallaci jumu’a na garin Azare.

Sannan ya ziyarci hubbaren sarakunan Katagum da suka gabata inda ya yi musu addu’a.

Sarkin Kano yayin ziyarar da ya kai masarautar Katagum

Meye dalilin ziyarar?
Maƙasudin ziyarar shi ne ƙara inganta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin yankunan, wadda ta samo asali tun daga tushe.

Labarai masu alaka:

Yadda Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Kano a fadar sa

Sarkin Kano ya nuna damuwar sa kan yadda rashin zaman lafiya ya dai-daita Arewa

Me sarkin Kano ya faɗa a ziyarar?

Yayin jawabin sarkin Kano a masarautar Katagum

Cikin jawabin da ya gabatar Alhaji Aminu Bayero ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar masarautar kan rashe-rashen da aka samu sanadiyyar annobar Corona.

Ya ce, cikin jerin ziyarorin da ya kai masarautu, wannan ita ce ziyarar da aka yiwa taron dangi na ‘yan uwa baki ɗaya.

Sarkin ya kuma yi godiya da irin karamcin da al’ummar masarautar Katagum suka nunawa sarki Sanusi na daya tun a wancan zamanin.

Abin da Sarkin Katagum ya ce a ziyarar

Sarkin Katagum Alhaji Umar Faruk na biyu, ya bayyana farin cikinsa.

Ya ce, ko a zamanin da jihar Kano ke maƙotaka da jihar Bauchi ba a taɓa jayayya kan iyaka tsakaninmu ba, wanda hakan ke nuna irin amincin da ke tsakani.

Mai martaba sarkin Katagum Alhaji Umar Faroq na biyu yayin ziyarar da sarkin Kano ya kai masa.

Abin da ya ƙarfafa dangantakar Kano da Katagum

Sarkin ya ce, daga cikin dalilan ƙarfafa aminci tsakanin masarautun akwai alakar auratayya da aka rika yi.

Kuma cakwai da yawa cikin mutanen masarautarsa da ke zaune a jihar Kano waɗanda sun samu karɓuwa saboda haka babu abin da zai cewa Kano sai godiya.

Masarautun da Sarkin Kano ya kai ziyara bayan naɗinsa

Hoton Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Sarkin Kano ya kai ziyarar karfafa dangantaka a masarautu daban-daban na faɗin kasar nan.

Daga cikin masarautun da ya ziyarta kawo yanzu, akwai fadar mai alfarma sarkin musulmi, da masarautar Gwandu, da ta Gusau, da kuma masarautar Ilorin ta jihar Kwara.

Sarkin ya kuma ziyarci masarautar Zazzau, da kuma masaurautu biyar na jihar Jigawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!