Kiwon Lafiya
Dantakarar gwamnan Ekiti ya shigar da kara Kayode Fayemi gaban kotu
Dantakarar gwamnan jihar Ekiti a jam’iyya APC Segun Oni ya shigar da wata kara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda yake kalubalantar tsayar da Kayode Fayemi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC da ta tsayar a zaben ranar 14 ga watan Yuli mai zuwa.
Oni ya shigar da wannan karar ne gaban babbar kotun tarayyar ta hannun lauyansa Gani Faniyi.
Kayode Fayemi wanda ya samu kuri’u 941 a zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta gabatar a ranar 12 ga watan Mayun da ya gabata ya samu nasara ne akan Oni wanda ya samu kuri’u 460.
Sai dai Oni ya bukaci kotu da ta tabbatar masa cewar ko ya halarta Fayemi ya tsaya takarar, duk da cewa a lokacin da a aka gudanar da zaben bai yi murabus daga kan mukamin sa na minista ba ko kuma aka sin haka.
Haka kuma ya bukaci kotun da ta tabbatar masa cewar ko bashi takarar ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma tsarin da jam’iyyar ta APC ke tafiya a kai.