Labarai
Daruruwan yan sanda na fuskantar barazanar kora ko rage musu matsayi

Daruruwan yan sanda ne ke fuskantar barazanar kora ko rage musu matsayi ke gaban kwamitin ladabtarwa na hukumar, bayan kafa kwamitin bincike a kansu.
Wannan na zuwa ne bayan da hukumar da sallami ‘yansanda 34 a baya-bayan nan, tun bayan da Kayode Egbetokum ya kama aiki a matsayin shugaban rundunar.
Yanzu haka dai akalla manyan jami’an yan sanda 151 daga bangarori daban-daban a fadin kasar nan ke gaban kwamitin ladabtarwa bisa zargin karya dokoki da nuna rashin kwarewa a bakin aiki daga jami’an.
Daily Trust ta rawaito cewa kwamitin ya fara zaman sa a Litinin din nan data gabata a shalkwatar ga hukumar dake Abuja inda kuma ake sa ran za a kammala shi cikin kwanaki 10 tare da tura sakamakon zuwa ga hukumar ta ‘yan sanda.
You must be logged in to post a comment Login