Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Daya daga cikin kwamishinoni a Gombe ya yi murabus

Published

on

Kasa da kwanaki 10 daya rage a gudanar da zaben gwamnoni, kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Gombe, Abishai M. Andirya, ya yi murabus.

Abishai Andirya, ya bayyana yin murabus din ne a jiya Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, ‘inda ya ce ya ajiye mukaminsa ne sakamakon shi kwamishina ne kawai a baki’.

A cewarsa, ‘tun da aka nada shi watanni uku da suka wuce, sau daya kawai ya gana da gwamnan shima a taron majalisar zartarwar jihar ne’.

A cikin kwafin takardar murabus din da jaridar Daily Trust ta samu, Andirya ya ce ‘ya yi murabus ne tun daga ranar 20 ga watan Fabrairun daya gabata’.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!