Kiwon Lafiya
Dino Melaye:Ya zargin kamfanin NNPC da bude asusu a bankin Keystone ba bisa ka’ida ba
Shugaban kwamitin kula da birnin tarayya Abuja na majalisar Dattawa Sanata Dino Melaye, ya zargi kamfanin mai na kasa NNPC, da cewa ya bude wani asusu ba bisa ka’ida ba; a bankin Keystone, wanda kuma ya yi ajiyar dala miliyan dari da talatin da bakwai a cikin asusun.
Sanata Dino Melaye ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar, ya na mai cewar kamfanin na NNPC ya sabawa doka wajen bude asusun a bankin maimakon ajiye kudin a babban bankin kasa CBN.
A cewar Dino Melaye, kamfanin NNPC ya bude wani bangaren kamfanin sa da ke aikin iskar Gas wanda wasu ‘yan kasar Italiya da Belgium da kuma Faransa ke da hannun jarin kaso hamsin na jarin kamfanin wanda kuma kudaden sa ne ake ajiyewa a asusun.
Sanata Dino Melaye ya kuma ce kamfanin na NNPC ya cire dala miliyan hudu cikin kudin ajiyar a baya-bayan nan.