Labarai
Doka ta soke yin kayan lefe a Kano
Binciken da Freedom Radio ta yi, ya gano cewa, tun a shekarar 1988 Gwamnatin mulkin soji ta wancan lokaci ta soke yin kayan lefe.
A zamanin mulkin Gwamnan Soja Wing Commander Muhammed Ndatsu Umaru ne, Gwamnatin Kano ta yi wata doka da ta haramta wasu tsarabe-tsaraben aure guda goma sha tara.
Abubuwan da dokar ta shafa sun haɗa da.
1. Gaisuwar Uwa da Uba.
2. Kayan Zance
3. Kayan Lefe
4. Kayan Baiko
5. Kayan Adala
6. Kuɗin Aure
7. Kuɗin Ƙunshi
8. Kuɗin Rigar Mijin Baya
9. Kuɗin Buɗar Kai
10. Kayan Buɗat Kai
11. Kuɗin Alibidi
12. Kuɗin Ƴan-Mata
13. Sayen Fura
14. Zaman Ajo
15. Sayan Baki
16. Kuɗin Kama Hannu
17. Garar Aure
18. Garar Haihuwa
19. Yinin Biki.
Ƙunshin wannan doka dai ya yi tanadin cewa, duk wanda ya saki matar sa, to za ta zauna a gidan sa har ta kammala idda kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.
Dangane da tsarin gudanar da bikin aure kuwa dokar ta yi tanadin cewa, ginshiƙan auren su ne sahalewar Gwamnati, da kuma shaidar Dagaci da ta Mai Unguwa sai iyaye da waliyai da kuma sadaki bisa dokar shari’a.
Barista Bashir Muhammad lauya ne mai fafutukar kare haƙƙin al’umma a nan Kano ya ce, kamata ya yi Gwamnati ta sake nazari domin sake aiwatar da wannan doka a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login