Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano za ta kashe sama da miliyan 98 a bangaren wasanni

Published

on

Majalisar zartarwa ta jihar Kano, ta amince da kashe naira miliyan 82, don siyan kayan wasanni ga kungiyoyin Kwallon kafa na jihar.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishin yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ya sanyawa hannu, inda sanarwar ta ce Majalisar ta amince da ware kudin tare da kashe su ne a yayin zaman da ta yi a larabar makon da ya gabata.

Majalisa ta amince Ganduje ya nada sabbin masu ba shi shawara

Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje

 Ta cikin Sanarwar, Muhammad Garba ya ce an ware kudin ne don siyan riguna da kwallayen kafa da sauran kayan amfani a bagaren na  tamola.

Malam Muhammad Garba, ya kara da cewa kayan za a rabawa kungiyoyi guda dubu daya da dari bakwai da casa’in da biyu dake fadin jihar Kano.

Ana sa ran ko wa ce kungiya zata samu rigunan kwallo da jakunkuna da littafin rubutu da kuma kwallaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!