Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dokar kafa hukumar bunkasa ilimi na jihar Kano ya tsallake karatu na 2

Published

on

Dokar kafa hukumar bunkasa harkokin ilimi ta jihar Kano ta shekarar dubu biyu da goma sha Tara ta tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin jihar Kano a yau Talata.

Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa haka Kuma kudirin dokar kafa sabbin masarautu guda hudu a jihar Kano Wanda gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya turo da shi a jiya an yi mishi karatu na farko.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar a yau, shugaban masu rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madari, ya ce kudirin dokar kafa hukumar bunkasa harkokin ilimi zai taimaka gaya wajen bunkasa harkokin ilimi a jihar Kano musamman ganin cewa za a rika cirar kaso biyar na kafatanin kudaden shiga na cikin gida da aka samu domin sawa cikin asusun yayin da Kuma kananan hukumomi za su ba da kaso biyu na kudaden d suke karba daga asusun tarayya.

A wani makamancin wannan labarin Kuma hukumar kula da ba da tallafi karatu ta jihar Kano ta bukaci majalisar dokokin jihar ta Kano da ta gaggauta sahalewa kudirin dokar kafa hukumar bunkasa harkokin ilimi ta jihar Kano Wanda gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya turo da shi.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Zakari Muhammed ne ya bayyana haka ya yin zantawa da manema labarai.

Majalisar dokoki za ta gyara dokar kafa hukumar samar da tallafin ilimi

Majalisar dokokin Kano ta katse hutun da take yi , zata dawo aiki gobe

Majalisar Kano zata aiwatar da dokar cin zarafin bil adama

Haka zalika Alhaji Abubakar Zakari Muhammed ya kuma ce nan ba dadewa ba jihar Kano za ta fara amfana da irin kudaden da gwamnati ke kushewa wajen tura ‘yan asalin jihar zuwa ketare domin karatu a jami’o’i daban-daban.

Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa shugaban hukumar kula da ba da tallafin karatu ta jihar Kano na cewa, daya daga cikin daliban jihar Kano da aka tura shi kasar Faransa tuni yayi fice sakamakon wata fasaha da ya kirkiro wadda za ta taimaka wajen dakile kutse da kuma ayyukan batagari a Internet.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!