Labarai
Majalisar Kano zata aiwatar da dokar cin zarafin bil adama
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za ta yi duk me yiwuwa don ganin an aiwatar da dokar hana cin zarafin bil adama da majalisun dokikin tarayya suka sahalewa tun a shekarun baya.
Akawun majalisar dokokin ta Kano Abdullahi Alfa ne ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi ga gangamin wata kungiya mai rajin yaki da cin zarafin mata mai suna ‘North Normal’ wadanda su ka hi wata zanga zangar lumana zuwa majalisar dokokin ta Kano da safiyar yau.
Ya ce majalisar a shirye take ta yi duk wata doka da za ta taimaka wajen dakile cin zarafin bil adama musamman mata da kananan yara.
Tun farko da take gabatar da jawabi daya daga cikin jagororin kungiyar Malama Zainab Nasir Ahmed ta ce sun zo majalisar da nufin neman goyon bayanta kan aiwatar da dokar yaki da cin zarafin bil adama wadda aka yi tun a shekarar dubu biyu da sha biyar a majalisun dokokin tarayya.
Acewar ta amma har ya zuwa wannan lokaci jihohi biyu ne kacal daga Arewacin kasar nan su ka aiwatar da dokar a jihohinsu.
Kano yara 9: taron wasu mata sun bukaci sa hannun majalisar Kano
Kai tsaye: An Kammala tantance sunayen kwamishinoni -Majalisar Kano
Majalisar yara na yaki da safarar kananan yara
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito kungiyar na cewa gangamin wani bangare ne na bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya wadda ke gudana a yau.