Connect with us

Labaran Kano

Majalisar dokoki za ta gyara dokar kafa hukumar samar da tallafin ilimi

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za tayi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da gyaran dokar kafa hukumar bunkasawa da kuma samar da tallafi  ga bangaren ilimi ta jihar Kano ta shekarar dubu biyu da goma sha tara wanda gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya turo da shi.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana haka yayin karanta wasikar da gwamnan Kano ya turowa majalisar game da gyaran kudirin dokar hukumar ta Kano state education development establishment support bill 2019.

Ya ce matukar aka amince da gyare-gyaren da aka yi ga hukumar aka kuma amince da shi akan lokaci zai bai wa jihar Kano damar fara cin gajiyar tallafi kan harkokin ilimi daga kungiyoyin ba da tallafi kan harkar ilimi a duniya.

Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, majalisar ta bukaci  sanya batun gyaran dokar cikin ayyukan da za ta gudanar a zamanta na gaba.

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!