Labaran Kano
Dokar masu bukata ta musamman za ta kare hakkinsu- Gwamna Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce, da zarar dokar masu bukata ta musamman ta fara aiki za ta maganace matsalar cin zarafinsu.
Haka kuma y ace dokar ta masu bukata ta musamman za ta kare yancin su.
Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman ta jihar Kano Alhaji Kabir Muhammad Tarauni ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce, tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta sahale dokar masu bukata ta musamman, aka fara nazarin yadda za a aiwatar da ita don amfanar mutane masu bukata ta musamman.
Ya kuma ce, a yanzu ana jiran gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin kula da aiwatar dokar sannan ta fara aiki.
You must be logged in to post a comment Login