Labarai
Dokar tanadin kalubalen lafiya da ka iya tasowa ta tsallake karatu na biyu
Dokar Tsaron ƙalubalen lafiya da ka iya tasowa ta Bana, ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin jihar Kano.
Dokar ta kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau ƙarƙashin jagorancin shugabanta Jibril Isma’il Falgore.
A zaman na yau, Ɗan majalisar dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai Dakta Musa Ali Kachako ne ya gabatar da karatu na biyu wanda bayan tattaunawa a tsakanin mambobin majalisar suka amince da karatun nasa.
A ganawar sa da manema labarai, Ɗan majalisar na Takai, ya bayyana wasu cikin alfanun da samar da dokar zai haifar.
A wani labarin kuma, majalisar ta buƙaci gwamnatin jiha da ta samar da tsaftataccen ruwan amfanin yau da kullum a yankin ƙaramar hukumar Tudun Wada.
Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Tudun Wada Sule Lawan ya gabatar yayin zaman na yau.
Ɗan majalisar ya ce, wahalar ruwa a yankin ta sanya har ana sayar da Lita 25 ta Ruwa a kan Naira 100.
You must be logged in to post a comment Login