Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun shirya magance matsalolin Muhalli a Kano- Muhammad S Khalil

Published

on

Hukumar dake kula da matsalolin da suka shafi zaizayar kasa hanyoyin ruwa da kuma dumamar yanayi ta jihar Kano tace a shirye take wajen ganin ta magance duk wani abu da ke kawo wa muhalli cikas a nan jihar Kano.

Shugaban hukumar Alhaji Muhammad Khalil ne ya bayyana haka yayin ziyarar gani da ido da ya kai wasu sassa na karama hukumar Ungogo.

Muhammad S Khalil ya kara da cewa ‘zaizayar kasa na faruwa ne ta dalilai biyu wanda ya haɗar da dabi’a Dan Adam da kuma daga Al…’.

Inda yace ‘ diban yashin da akeyi a wannan yankin, ya taka rawa matuka wajen haifar da zaizayar kasa a yankunan’.

Ya kara da cewa gwmanatin jihar Kano a shirye take wajen gani ta fara aikin gyare-gyare wannan wuraren da zaizayar kasa ta cinye’.

A hannu guda Kuma mazauna wannan yanki sun bayyana cewa ‘wannan wuri dake da zaizayar kasa na haddasa musu asara rai da kuma dukiya’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!